Home History Tarihin Nupe (Nupe History In Hausa Language)

Tarihin Nupe (Nupe History In Hausa Language)


Tarihin Nufawa A Najeriya

Tarinhin Nupe, Nufe, Nufawa, Banufe, Asalin, Kasar, HistoryYadda Kabalir Nupe Suka Fara Rayuwa Bayan Isowarsu A Kasar Najeriya Da Kasashen Su

Nupe wasu kabilu ne da suke rayuwa a tsakiyar najeria kamar su Niger state, Kwara state, Kogi state da Abuja, Hausawa suna kiransu da suna Banufe (Singular) ko Nufawa wato (Plural) wato masu yawa kenan.
Makopcin su Gwarawa suna kiran da suna Anupeyi, kuma Yarbawa suna kiran su da suna Tapa (Takpa).
Akwai wasu yaruruka sama da biyar wadda suke karkashin Nupawa wato Kakanda, Dibo, Kupa, Gana Gana, Bassa Nge (Nupe Tako) wato su napawa na kudu masu zama a kasar Kogi.

Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa ‘Tarihi da Al’adun Mutanen Najeriya’ cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bida, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.

Amma binciken Dr. Sidi Tiwugi Shehi ya kawo ra’ayoyin masana da yawa saɓani da wannan. Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Ukba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabci tare da zama a ƙasar Nupe.

Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara. Shi kuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu) Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna ‘Social Symbiosis and Tribal Organisation’.

Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata. Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka kafa birnin Kutigi.

Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.
Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nupe.

Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nupe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S. Wannan yasa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nigeria, sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamirai, Nupawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbagyi.

Alƙalin Gwari Ummaru ya ruwaito cewa Farkon labarin Fulanin Nufe ya soma ne da Malam Dando, wanda yazo ƙasar Nufe daga ƙasar Hausa. An ce shi mutum ne matsakaici wajen tsawo da haske, bashi da kaurin jiki kuma. Ya iske Nufe a zamanin da Sarki Majiya ke mulki. Sai ya zama almajirin sa. A zamanin da Malam Dando yazo ƙasar Nufe yana da ƴaƴa uku, Majigi, Abdu Ɓuya, da Etsu Usmanu. Ya rinƙa yawo garuruwan Nufe yana wa’azi har ya isa Daba.

A wannan garin kuwa akwai wata mahaukaciya tana ɗaure cikin mari, ana kiranta da suna Fatsumako. Masu magani sunyi har sun gaji ba tare da ta samu sauƙi ba. Rannan Malam Dando na shigewa inda take sai tayi ƙara har ya jiyo muryar ta, sai ya tambaya “wanene yake ƙara haka?” sai akace masa “Wata mahaukaciya ce wadda masu magani suka kasa warkad da ita.”

Sai Malam Dando yace “Ku bani ita ina warkad da ita, in Allah ya yarda”. Da waliyanta suka ji sai suka amsa masa da cewa “Mun baka ita”. Malam Dando ya koma gida ya yi rubutu a alluna biyu, ya wanke, ya zuba a cikin ƙoƙuna biyu ya aika musu. Yace ƙwarya ɗaya ayi mata wanka da ita. Ɗayar kuwa a bata tasha. Sannan ya haɗa musu da turare na hayaƙi da za a yi mata turare dashi.

Iyayenta suka aikata kamar yadda manzon Malam Dando ya sanar musu. Da aka kwana uku sai Malam Dando ya tafi don ya ganta, sai yace da iyayen ta “ku kwance mata marin nan”. Iyayenta suka yi wa Malam Dando musu kaɗan, sa’an nan suka yarda suka kwance ta. Malam Dando ya kaita cikin kafe yace ta zauna nan. Daga baya sai ya nemi aurenta suka amince masa, bayan sunyi aure ya tafi da ita Juguma suka kwana ɗaki ɗaya. Daga nan bata sake komawa cikin halin hauka ba. Ta sami cikin ɗa Mustafa, sannan ta haifi Muhammadu Saba.

A zamanin da ta haifi Muhammad Saba sai sarki Majiya Zubairu yace yana sonsa, don haka abar shi a hannun sa ya girma. Akwai wata rana da Sarki Majiya ya shirya zuwa yaƙi Kukuku, Malam Dando ne ya bashi asiri ya kai ya zuba acikin ƙasar, sannan yaci su da yaƙi ya samu dukiya mai tarin yawa. Daya komo gida sai ya aikewa Malamin kuyangi guda biyu a matsayin kyauta.

Malam Dando ya karɓe su yayi godiya, ɗaya ya mayar da ita sa ɗakan sa, ita ce Habibatu, ɗaya kuma ya aikewa Atiku ɗan Shaihu Usmanu, hasken zamani, kogin talikai, babban waliyi, itace ta haifi Ummaru Nagwamatse. Wannan duk anyi shine bayan rasuwar sarkin Musulmi Muhammad Bello ɗan Shehu Usmanu Ɗan Fodio.

Sana’ar Nupawa

Sana ar Nufawa, Nupe, Gona, Matan, History

Yawancin Nupawa Manumi ne wasu kuma suna aikin gomnati kamar Deputy Govenor na Central Bank Aisha Ahmad Ndanusa, IGP Ibrahim Idris Kpotun wanda yayi retire a shekarar 2016.
Nupawa anfi sanin su da numar shinkafa da doya da wasu kuma kama kifi ne sana ar su a wuraran River Niger.

Share It To Your Friends:👥